Monday 15th of December 2025
No record found
Entertainment / 2025-05-17 21:07:22

ME YA SA BA MA JIN WARIN TUSÁR MU?

Daga shafin Facebook na Ja afar A Sarki


Dabi atan jikinmu yakan fitar da iska imma ta baki, a matsayin gyatsa ko kuma ta dubura (anus) matsayin tusá (farting).


Shin ka san dalilin da yasa kake fitar da iska mai wari (smell)?  Sannan mai yasa idan kai kayi baka damuwa da warin abinda kai ka fitar?


Ita wannan iska kana haɗiyar (swallow) tane a yayin da kake cin abinci, da lokacin da kake magana. Sannan akwai wasu abubuwa daban dake ƙara yawa iskar da kake haɗiya, kamar shan lemon kwalba (fizzy drinks), cin abinci da sauri, ko tsotsar wani abu, kamar pen, finger, dss. To wata daga wannan iska wacce ta samu tsayawa iya ciki (stomach) na fita daga jikinmu a matsayin gyatsa (burps), wata kuma sai ta samu wucewa har zuwa babban hanji (lange intestines). To akwai bacteria waɗanda ke zaune a gut ɗin mutum, a yayin da suke cin abinci a cikin hanjin mutum, sukan  samar da iska mai wari (stinky air) wacce idan ta fito ke da wari wacce ake kira "Tusá".


Akwai nau in abincin da cinsa ke ƙaruwar yawan yinta da mai da ita (a lot stinkier). Cin wake (beans), chickpeas, cabbage, sprouts, albasa (onions) da nama (meat), duk waɗannan nau in abinci suna dauke da sinadaran (chemicals) dake sanya fitar da iska mai wari (stinky air).


Dalilin daya sa baka jin warin farts ɗin ka shine, watakila saboda kwakwalwar ka ta saba da warin jikin ka (body odours), to hakan sai yai making farts din ka less offensive. Sannan kuma olfactory system din jikinka yakan sabawa (adapting) da irin warin da kake ji kullum, ta yadda hakan ba zai saka jin munin warin ba kamar yadda kake ji daga wani.


Haka kuma daga dalilan rashin damuwa da farts din da mutum yayi akwai psychological comform in your own biology - saboda ai abinda ya fita daga jikinka is an extension of you, to sai hakan ma ya sa rashin jin offensiveness na farts din daka fitar.


Fassara ce daga littafin Dr Adam Kay (Kay s Anatomy).

440 0

Comments

Leave a comment

Newsletter

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Kayi rajista

Muhimmai

Business / 2024-12-07 21:43:09
Reps Inuwa Garba Sympathi
Business / 2024-12-07 07:41:43
NOA Sensitize Nigerians
Business / 2024-11-10 07:30:26
North-Eastern University
Business / 2024-11-04 00:18:00
Editors Conference: Shet
Business / 2024-10-29 21:29:43
Gombe Reps Empower 150 Yo

Gombe Reporters

Gombe Reporters is an online channel based in Gombe.....

Quick Links

© Gombe Reporters.. All Rights Reserved.